Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta yi kakkausar suka ga wani rahoton BBC da aka wallafa a ranar Laraba mai taken "Har yanzu Muna Yaki... Kurdawan Siriya Suna Yakar Turkiyya Watanni Bayan Tumɓuke Assad."
Hukumar ta bayyana cewa ikirarin da aka yi a cikin labarin yaudara ne, mai ɓangare daya, kuma ba ya nuna gaskiya game da ayyukan yaki da ta'addanci na Turkiyya a arewacin Siriya.
Gwamnatin Turkiyya ta yi gaggawar shiga tsakani ta hanyar yin gyara ga gidan kafar watsa labaran ta Birtaniya, yayin da ita ma cibiyar yaki da yada labaran karya ta fitar da sanarwa kan lamarin.
A nata martanin, Turkiyya ta jaddada cewa ayyukan da sojojinta ke yi a Siriya suna kai harine kan kungiyoyin ta'addanci irinsu PKK/YPG da Daesh ba wai wata kabila ko fararen hula ba.
Sanarwar ta kara da cewa "Manufar Turkiyya kawai ita ce ta tinkarar kungiyoyin 'yan ta'adda da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin, kasarmu ba ta shiga wani rikici da ya danganci kabilanci ba, haka kuma ba ma kai wa fararen hula hari."
'Aikin yaki da ta'addanci ba rikicin kabilanci ba'
Tun bayan barkewar rikicin Siriya, Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a arewacin Siriya da kuma hana yaduwar kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin.
Rundunar sojan Turkiyya ta gudanar da ayyukan kan iyaka a karkashin dokokin kasa da kasa, da nufin tabbatar da tsaron iyakokinta da kuma tabbatar da tsaron ‘yan Syria da suka rasa matsugunansu.
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta soki rahoton na BBC da yin kuskuren bayyana wadannan yunƙurin, tana mai cewa labarin karyar na BBC ya kwatanta Turkiyya a matsayin mai yaƙi da Kurdawa.
Sanarwar ta ce "Rahotan BBC na kokarin haifar da wata fahimta ta ƙarya da cewa Turkiyya na yaƙi da Kurdawa a Siriya. Turkiyya tana goyon bayan yankin Siriya kuma ta daɗe tana goyon bayan zaman lafiya a tsakanin al'ummarta."
"Ba kamar PKK/YPG ba, wadda ta shiga tarihi kan abin da ya shafi ayyukan tilastawa, da kawar da wasu ƙabilu, da kai hare-hare kan fararen hula, Turkiyya na ba da fifiko ga kare fararen hula a ayyukanta."
A matsayin shaida na jajircewarta kan ayyukan jinƙai, Turkiyya ta ba da misali da yadda ta ba da mafaka ga miliyoyin Siriyawa, da suka hada da dubban Kurdawa da suka tsere wa zalunci a karkashin hambararriyar gwamnatin Asad.
'Aikin yaki da ta'addanci ba rikicin kabilanci ba'
Tun bayan barkewar rikicin Siriya, Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a arewacin Siriya da kuma hana yaduwar kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin.
Rundunar sojan Turkiyya ta gudanar da ayyukan kan iyaka a karkashin dokokin kasa da kasa, da nufin tabbatar da tsaron iyakokinta da kuma tabbatar da tsaron ‘yan Syria da suka rasa matsugunansu.
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta soki rahoton na BBC da juya zance da karkatar da hankulan mutane wajen bayyana wadannan yunƙurin, tana mai cewa labarin na ƙarya ya kwatanta Turkiyya a matsayin yaƙi da Kurdawa.
Sanarwar ta ce "Rahotan BBC na kokarin haifar da wata fahimta ta karya da cewa Turkiyya na yaki da Kurdawa a Siriya. Turkiyya tana goyon bayan yankin Siriya kuma ta dade tana goyon bayan zaman lafiya a tsakanin al'ummarsa."
"Ba kamar PKK/YPG ba, wadda ke da tarihin ayyukan tilastawa da rikicin kabilanci, da kai hare-hare kan fararen hula, Turkiyya na ba da fifiko ga kare fararen hula a ayyukanta."
A matsayin shaida na jajircewarta kan ayyukan jinƙai, Turkiyya ta ba da misali da yadda ta ba da mafaka ga miliyoyin Siriyawa, da suka hada da dubban Kurdawa da suka tsere wa zalunci a karkashin hambararriyar gwamnatin Asad.
Barazanar PKK/YPG ga zaman lafiyar Siriya
Turkiyya ta kuma yi gargadin cewa babbar barazana ga sabuwar gwamnatin Siriya wacce aka kafa bayan rugujewar gwamnatin kasar ita ce kasancewar kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG.
Sanarwar ta kara da cewa, "Wannan kungiyar ta 'yan ta'adda tana yin illa ga hadin kan kasar Siriya, tana kuma haifar da rarrabuwar kawuna na ƙabilanci, da kuma neman kafa haramtacciyar kasa ta hanyar tashin hankali.
"Irin wadannan ayyuka ba wai kawai barazana ce ga makomar Siriya ba, har ma da babban tsaron yankin."
Turkiyya ta sha yin kira ga kasashen duniya da su amince da kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG a matsayin mai barazana ga tsaro, inda ta bayyana cewa ayyukanta sun wuce kasar Siriya kuma suna yin tasiri ga tsaron kasar Turkiyya.
Ankara ta ba da shaidar cewa kungiyar na amfani da farar hula a matsayin garkuwa da kuma tilasta daukar yara— zarge-zarge da tuni aka shigar da su cikin rahotan kare hakkin bil adama na kasa da kasa.
Yakin da Turkiyya ke yi da Daesh da hadin gwiwar kasa da kasa
Har ila yau Ankara ta jaddada rawar da take takawa a yakin da ake da Daesh a duniya, inda ta yi nuni da cewa ayyukan soji a kasar Siriya sun yi daidai da manufofin kawancen kasa da kasa na yaki da ta'addanci.
Sanarwar ta ce "Turkiyya na daya daga cikin kasashen da suka fi tasiri wajen yaki da Daesh, tare da kawar da dubban 'yan ta'adda da kuma tabbatar da tsaro a yankin."
"Mun kuma ba da kariya ga dubban fararen hula da suka tsere daga rikicin Daesh tare da tallafa wa ayyukan jinƙai na sake gina yankunan da abin ya shafa."
Idan aka yi la’akari da irin kokarin da Turkiyya ke yi na yaki da ta’addanci, Ankara ta soki BBC da wallafa abubuwan da ta kira “karkatar da kai da son zuciya”.
"Muna sa ran BBC za ta bi tsarin aikin jarida mai inganci da bangarori da dama maimakon yada rahotannin da ba su dace ba," in ji sanarwar.