Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa sun yi tur da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan ba da shawarar cewa a samar da ƙasar Falasɗinawa a yankin Saudi Arebiya.
Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit a ranar Lahadi ya ce yin tunani ma kan kalaman Netanyahu abu ne da ba za a yarda da shi ba kuma bai yi daidai da gaskiya ba, yana mai cewa irin waɗannan shawarwari ba komai ba ne illa zarmewa da yaudarar kai.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta jaddada cewa tana “watsi da waɗannan kalamai da ke neman janye hankalin mutane daga munanan ayyukan da Isra’ila ke cigaba da yi na mamaya da zaluntar ‘yan’uwa Falasɗinawa a Gaza.”
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ji daɗin “Allah wadai da ƙin amincewar da sauran ƙasashe ‘yan’uwanmu suka yi kan abin da Benjamin Netanyahu ya bayyana a matsayin korar al’ummar Falasɗinu.”
Kalaman Netanyahu, waɗanda wasu kafafen watsa labaran Isra’ila suka bayyana a matsayin raha, sun zo ne a daidai lokacin da tuni yankin ke cikin ruɗu saboda shawarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ta cewa zai karɓi yankin Falasɗinu, da ke nufin korar al’ummar Gaza.
'Kasa mai yawa'
A wata hira da Netanyahu da aka nuna a talabajin a ranar Alhamis, ɗan jaridar Isra'ila mai tsaurin ra'ayi Yaakov Bardugo ya bijiro da batun yiwuwar shiryawar diflomasiyya da Saudiyya, inda har ya ɗan yi tuntuɓen harshe a lokacin da yake son faɗar matsayar Riyadh ta cewa ba za a cim ma wata matsaya ba "in ba a samar da ƙasar Saudiyya ba."
Sai Netanyahu ya ci gyaransa da cewa "ko dai ƙasar Falasɗinu?", inda ya ƙara da cewa "Sai dai idan so kake a samar da ƙasar Falasɗinu a cikin yankin Saudi Arebiya ... Ai su 'yan Saudiyya suna da ƙasa mai yawa da faɗi sosai."
Firaministan Isra'ila ya ci gaba da bayyana tattaunawar da aka yi kafin yarjejeniyar Abraham, inda wasu kasashen Larabawa suka daidaita alakarsu da Isra'ila, inda ya kammala da cewa: "Ina ganin ya kamata mu bar wannan tsari ya dauki matakinsa."
Sai dai shawarar samar da kasar Falasdinawan a wajen Gaza da kuma Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya haifar da tofin Allah tsine a yankin, ciki har da Qatar da Masar da ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu, wadanda suka bayyana kalaman a matsayin "wariyar launin fata".
Keta dokokin ƙasa da ƙasa
Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Jordan ta yi Allah wadai da kalaman tana cewa "masu tada hankali ne da kuma keta dokokin kasa da kasa ƙarara", tana mai jaddada cewa Flasdinawa na da "yancin kafa kasa mai cin gashin kanta" tare da Isra'ila.
Ma'aikatar harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah-wadai da kalaman Netanyahu da cewa "abin zargi ne da tsokana," tana mai cewa "take dokokin kasa da kasa ne ƙarara da kuma na yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya."
Ga Falasdinawan, duk wani yunƙuri na tilasta musu ficewa daga Gaza zai haifar da baƙin ciki na tunawa da ranar "Nakba," ko ranar bala'i, wanda ke bayyana yawan gudun hijirar Falasdinawa a lokacin ƙirƙirar Isra'ila a 1948.
A cikin sanarwar da Saudiyya ta fitar, ta ce, "wannan tsattsauran ra'ayi na mamaya, tunani ne da bai fahimci abin da samar da kasar Falasdinu ke nufi ba" ga Falasdinawa ba.
Irin wannan tunani, in ji shi, ya hana al'ummar Falasdinu 'yancinsu "na rayuwa tun farko, kamar yadda ta lalata Gaza gaba daya" tare da kashe dubban mutane "ba tare da jin tausayin wani dan'adam ba ko kadan."