Kasuwanci
2 minti karatu
Ghana ta samu Cedi biliyan 294 daga kasuwanci a shekarar 2024
Zinari ne abin da ya fi samar wa ƙasar Ghana kuɗin shiga daga ƙasashen waje inda ya ba da gudunmawar da ta kai kashi 53 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta.
Ghana ta samu Cedi biliyan 294 daga kasuwanci a shekarar 2024
Hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce ana samun sauyi a fagen cinikayyar ƙasar: Hoto/Ghana News Agency
February 27, 2025

Ƙasar Ghana ta samu cedi biliyan 294.9 kan kayayyakin da ta fitar idan aka kwatanta da cedi biliyan 250.2 ta kashe kan ababen da sayo daga ƙasashen waje a shekarar 2024.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ruwaito cewa ƙasar ta samu rarar cedi biliyan 44.7 wanda ke daidai da dala miliyan 288, bisa alƙaluman cinikayyar ƙarshen shekarar 2024 da hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar.

Zinari ne abin da ya fi samar wa ƙasar kuɗin shiga daga ƙasashen waje inda ya ba da gudunmawar da ta kai kashi 53 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta.

Man da ƙasar ke fitarwa ne ya zo na biyu inda ya samar wa ƙasar kashi 17.8 cikin 100 na kuɗin shiga yayin da koko da ababen da ake samarwa daga koko ya ba da gudunmawar kashi 8.4 cikin 100 na kuɗin shiga.

Kamfanin dillancin labran ƙasar ya ambato shugaban hukumar ƙididdiga ta ƙasar wadda ta fitar da rahoton, Farfesa Samuel Kobina Annim, yana cewa rahoton ya nuna sauyi a cinikayyar ƙasar da ƙasashen Afirka inda ababen da ƙasar ke fitarwa ke kusan ruɓanya ababen da ta ke shigowa da su.

Ya ƙara da cewa rahoton ya nuna yadda ƙasar ke faɗaɗa cinikayya a kasuwar duniya.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us