Ɗan wasan Nijeriya, Ahmed Musa ya nemi a yi bincike kan mutuwar tsohon ɗan wasan Super Eagles, Abubakar Lawal a Uganda.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed Musa ya nemi gwamnatin Nijeriya da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, NFF su yi bincike tare da gwamnatin ƙasar Uganda domin neman haƙƙin Lawal.
Ahmed Musa ya nuna damuwa kan rahotanni masu karo da juna game da rasuwar ɗan wasan inda wasu rahotannin ke cewa ya mutu ne sanadiyyar hatsari yayin da wasu ke cewa faɗowa ya yi daga bene.
“Rahotannin masu karo juna na nuna cewa akwai alamar tambaya game da mutuwarsa kuma na tuntuɓi hukumomin Nijeriya da kuma hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya inda na ja hankalinsu game da wannan batun mutuwar,” in ji Ahmed Musa.
Kazalika hukumar NIDCOM da ke kula da ‘yan Nijeriya da ke ƙetare ta buƙaci mahukunta a Uganda da su yi bincike game da rasuwar ɗan wasan.
Wata sanarwar da shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa ta fitar ta ce akwai alamar tambaya a rasuwar ɗan wasan, tana mai cewa bai kamata a yi ɓoye-ɓoye game da shi ba.
“Gwamnatin Nijeriya za ta tabbatar tare da ganin an gudanar da cikakken binciken da zai tsage gaskiyar abin da ya faru,” in ji ta.