Nijeriya
2 minti karatu
Ficewar ƙasashen Sahel Alliance daga ECOWAS na shafar aikinmu — Rundunar Sojin Saman Nijeriya
Shugaban Sojin Sama na Nijeriya Air Marshal Hassan Abubakar ya buƙaci jami’an sojin saman Nijeriya su ƙara jajircewa da kuma amfani da dabaru wurin ganin sun cike giɓin da dakarun Burkina Faso da Nijar da Mali suka bari ta ɓangaren tsaron.
Ficewar ƙasashen Sahel Alliance daga ECOWAS na shafar aikinmu — Rundunar Sojin Saman Nijeriya
Air Marshal Hassan Abubakar ya ce ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS na kawo cikas ga aikinsu na tsaro. / Hoto: NAF
27 فبراير 2025

Shugaban Sojin Sama na Nijeriya ya ce ficewar ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso daga ECOWAS na shafar aikinsu na haɗin gwiwar soji a yankin Sahel inda ya ce a halin yanzu duk wani nauyi ya rataya a wuyan sojojin Nijeriya.

Air Marshal Hassan Abubakar a yayin wata tattaunawa da manyan hafsoshin sojin Nijeriya a Abuja, ya bayyana cewa janyewar ƙasashen ya mayar da hannun agogo baya ta ɓangaren tsaron iyakokin yanki musamman a ayyukan Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa ta Kasashen Yankin Tafkin Chadi wadda ke taka muhimmiyar rawa a yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Nijeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

Air Marshal Abubakar ya kuma yi gargaɗin cewa sakamakon barazanar da Chadi ke yi na ficewa daga rundunar ta Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa ta Kasashen Yankin Tafkin Chadi, hakan zai ƙara raunana ayyukan rundunar da kuma ƙara nauyin ayyukan rundunar kan Nijeriya.

Haka kuma ya yi gargaɗin cewa sakamakon wannan rashin jituwa tsakanin ECOWAS da waɗannan ƙasashe, ƙungiyoyin ta’addanci da ke da alaƙa da Al-Qaeda na amfani da wannan damar domin ƙara ƙarfi.

Ƙasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar waɗanda makwabtan Nijeriya ne sun shafe shekaru suna fama da matsalolin tsaro.

Haka kuma hare-haren ‘yan bindiga da kuma na ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi na ƙaruwa a arewacin Nijeriya waɗanda ta nan ne waɗannan ƙasashen na Sahel Alliance ke da iyaka da Nijeriya.

Sai dai a yanzu bayan raba gari da suka yi da ECOWAS, manyan jami’an tsaron Nijeriyar na ganin an tilasta musu gudanar da wannan jan aikin ba tare da haɗin kan sauran ƙasashen uku ba.

Wannan ne ma ya sa Air Marshal Abubakar ɗin ya buƙaci jami’an sojin saman Nijeriya su ƙara jajircewa da kuma amfani da dabaru wurin ganin sun cike giɓin da dakarun waɗancan ƙasashen suka bari ta sha’anin tsaron.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us