Yadda wasu 'yan wasan kwallo ke tunawa da asalinsu a Afrika
Wasanni
3 minti karatu
Yadda wasu 'yan wasan kwallo ke tunawa da asalinsu a AfrikaShahararren ɗan wasan damben boksin ɗan asalin Kamaru, Francis Ngannou ya mika wa ɗan wasan gaba na Real Madrid, dan asalin Brazil, Vinicius Jr, goyon gayyatar zuwa Kamaru.
#MQO69 : Football: <span lang="ha">Takar Cin Kwallon Kafa na UEFA Champions League</span>
22 Ianuarie 2025

Dan wasan boksin din ya wallafa wani hoto a shafinsa na X sanye da jesi din Kamaru mai lamba 7, wadda aka rubata sunan Vinicius, tare da saƙo mai cewa, “ɗan’uwa Vinicius Jr muna zumuɗin zuwanka gida.

Me ya sa Francis ya kira Vinicius dan-uwa, har yake fatan ya zo Kamaru?

Ga yadda batun ya samo asali. Hukumar ƙwallon ƙafar Brazil ce ta yi wani bincike, tare da haɗin gwiwar wata cibiyar gano mutane masu tsatson Afirka (African Ancestry).

Binciken ya gano cewar Vinicius tsatson ƙabilar Tikar ne, wadda wata fitacciyar kabila ce a Kamaru. Da yake magana game da tushensa, Vinicius ya ce, “Gano cewa tsatsona a Kamaru yake, lokaci ne na musamman a gare ni da iyalina.”

Domin girmama asalinsa, Vini ya sanya riga ta musamman mai ɗauke da tutocin Brazil da Kamaru a wasan da suka buga da Uruguay a makon jiya, inda aka tashi kunnen doki 1-1.

Da ma dai akwai ’yan wasa da dama da suka shahara wadanda a yanzu ‘yan kasashe da ke wajen nahiyar Afirka. Amma kuma tushe ko asalinsu a Afirka yake, kuma yawancinsu ba su manta da gida ba.

Bari mu duba wasu daga cikinsu.

Abokin wasan Vinicius a Real Madrid, wato dan wasan gaba dan asalin Faransa Kylian Mbappé, shi ma dan asalin Kamaru ne. Kuma da alama bai manta da gida ba, saboda dan wasan ya kai ziyarar kwanaki uku Kamaru a shekarar 2023, inda har ya ziyarci kauyen da aka haifi mahaifinsa, da wasu makarantu da ya gina a kasar.

Sannan akwai dan wasan gaba na Arsenal da ke buga wa kasar Ingila, Bukayo Saka, wanda asalinsa tsatson Nijeriya ne, kuma a watan Fabrairun da ya wuce ya dauki nauyin tiyatar da aka yi wa wasu yara marasa galihu su 120 a Nijeriya.

Haka nan, Bukayo Saka ya kai ziyara birnin Legas a watan Yulin shekarar 2023, inda wani bidiyonsa sanye da farin kaftani ya riƙa yawo a intanet.

Idan muka sake komawa Faransa, fitaccen dan wasa da shi ma bai manta da asalinsa ba shi ne Paul Pogba, wanda shi ma ya kai ziyara kasarsa ta asali wato Guinea Conakry, sanye da tufafin Afirka a shekarar 2023.

Dan wasan ya kuma buga wani wasan tara kudi don ayyukan jin-ƙai, wato Charity match yayin ziyar tasa.

Shi ma tsohon dan wasan tsakiya na tawagar Faransa da Arsenal, Patrick Vieira, bai manta da asalinsa ba, saboda kimanin shekara 20 da suka wuce ya gina wata katafariyar makarantar horar da kwallon kafa a Senegal, inda can ne tsatsonsa.

A yanzu dai da ake batun Vinicius ya gano tsatsonsa na Kamaru, al’ummar Kamaru da makwabtanta za su zuba ido su ga ta wace hanya dan wasan zai nuna cewa bai manta da asalinsa ba.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us