Yadda juriyar rediyo ke sa yake cigaba da zama ruwan dare a Afirka
Yadda juriyar rediyo ke sa yake cigaba da zama ruwan dare a Afirka
Tabbas har yanzu rediyo yana jan zarensa a faɗin Afirka, inda mutane ke sauraronsa saboda shirye-shirye masu nishaɗantarwa da labaran da suka shafe su kai tsaye - ciki har da na sauyin yanayi.
21 Shkurt 2025

Daga Charles Mgbolu

Alamar ja da aka rubuta 'On Air' a jiki ta kunnu a lokacin da Micah Sunday, ɗan jarida mai aiki a gidan rediyon Rhythm FM ya shiga cikin sutudiyo don fara gabatar da shiri.

Yana da minti 45 don karanto labaran duniya da rahotanni na wanan ranar.

Za ku yi tsammanin zai zo a gaggauce, amma Mikah ba ya cikin gaggawa. Rana ce irin wacce ya saba yi a ofis.

Rhythm FM ya kasance gidan rediyo mai zaman kansa da yake tashi sosai a Nijeriya, saboda kasancewar yana gabatar da shirye-shirye masu jan hankalin mai sauraro, duk da cewa kuwa ana cikin zamanin dijital ne.

Tabbas har yanzu rediyo yana jan zarensa a faɗin Afirka, inda mutane ke sauraronsa saboda shirye-shirye masu nishaɗantarwa da labaran da suka shafe su kai tsaye - ciki har da na sauyin yanayi.

An yi bikin Ranar Rediyo ta Duniya ran 13 ga watan Fabrairu, inda take ranar ya kasance "Rediyo da Sauyin Yanayi", kuma tashoshi a fadin Afirka sun yi bikin wannan rana.

An yi bikin Ranar Rediyo ta Duniya ran 13 ga watan Fabrairu.

A cikin shirin da Micah ya gabatar a wannan rana ya tattauna da masu fafutukar sauyin yanayi don tattauna wannan batu mai muhimmanci da wayar da kan masu sauraro.

Kayode Bakerr, shugaban gidan rediyon Rhythm FM, ya ce rediyo yana ta muhimmiyar rawa wajen sanar da ilimintar da masu saurare, musamman a yankunan da suke cikin surƙuƙi.

“Yawancin yankunan karkara har yanzu sun dogara da rediyo sosai saboda intanet bai je musu ba, kuma yawancin mutane ba su da wayoyin zamani. Rediyo na taimakawa wajen toshe gibin samun bayanai masu muhimmanci,” Bakerr ya shaida wa TRT Afrika.

Abu mai muhimmanci har a yanzu

A matsayin girmamawa ga tasirin wannan kafar sadarwa, UNESCO ta assasa ranar rediyo ta duniya a cikin 2011.

Kayode Bakerr, shugaban gidan rediyon Rhythm FM, ya ce rediyo yana ta muhimmiyar rawa wajen sanar da ilimintar da masu saurare. Bakerr/ Instagram  

Babban Zauren MDD ya amince da ita a matsayin ranar tunawa a duniya, a shekarar da ta biyi baya, tare da wata sanarwa da ta yaba wa rediyo a matsayin wata hanya mai karfi wacce ta cancanci yabo a ƙoƙarin wayar da kan ɗan'adam.

A cikin yanayin kafofin watsa labarai na Afirka, rediyo na ci gaba da haɓaka da isa ga mutane duk da karuwar barazanar daƙile shi da shaharar kafofin watsa labarun intanet da kuma samuwar AI.

Dangane da binciken da Jami'ar Oxford ta buga a cikin 2024, rediyo ya zama sananne bayan ƙarni guda da bayyanarsa a nahiyar Afirka wanda yanzu yana da "babban tasiri a duniya".

Cibiyar bincike ta Afrobarometer, ta bayar da rahoton cewa, kashi 68 cikin 100 na ‘yan Afirka ne ke samun labaransu daga gidajen rediyo a kullum ko kuma mako-mako, yayin da kashi 53 cikin 100 ne kawai ke samun labaransu daga gidajen talabijin, kashi 37 kuma daga hanyoyin intanet.

Binciken ya kuma yi nuni da cewa rinjayen rediyo bai takaita ga kasashen da ke da karancin hanyoyin shiga intanet ba.

Har ila yau, ya ba da misali da wani bincike da ya gano kashi 80% na 'yan Afirka ta Kudu na sauraron rediyo akalla sau ɗaya a mako a cikin ƙasar da kafofin watsa labaru na zamani ke da tushe mai girma.

Yaƙar labaran ƙarya

Ga Moses Umanah, shugaban sashen shirye-shirye na gidan Talabijin din Silverbird da ke Legas, kafofin yada labarai na al'ada kamar rediyo, na iya taimakawa wajen yaƙar labaran ƙarya.

Koyaya dai, akwai kyakkyawan fata ga rediyo da makomarsa a matsayin babbar hanyar yada bayanai. Hoto : Reuters

Umanah ya shaida wa TRT Afrika cewa "Yayin da labaran ƙarya ke yaduwa cikin sauri a ko yaushe, rediyo kayan aikin tantancewa ne saboda labarin kan fito ne daga wani mutum da aka san sunansa da muryarsa ba kamar na intanet ba da ake yada ƙarya daga wajen wanda ba a ma san waye ba."

Duk da haka, shugabannin gidajen rediyo da masu watsa shirye-shirye sun yarda cewa kafofin watsa labaru na gargajiya na ci gaba da fuskantar barazana saboda zuwan kafofin watsa labarai na zamani wadanda ke da miliyoyin masu amfani da su.

Har ila yau, bincike ya nuna gagarumar gasa daga manyan dandamali na dijital kamar su podcast, wanda ya sami ci gaba mai ma'ana a nahiyar a cikin 'yan shekarun nan.

Dangane da shafin intanet mai bincike na Statista, ana sa ran kasuwar podcast a Afirka za ta sa yawan masu amfani da shi su kai miliyan 35.7 nan da shekarar 2029.

Babban kalubale ga rediyo shi ne jawo hankalin matasa masu sauraro.

Micah Sunday ya ce ana iya auna tasirin rediyo ta hanyar la'akari da mutanen da ake yawan gayyata don yin magana a cikinsa.

"Galibin wadanda suke shiga rediyo su yi magana 'yan fiye da 30 ne. Hakan na nuna cewa rediyo yana rasa abokan hulɗa matasa waɗanda suke samun bayanai daga shafukan intanet irin waɗanda ba za su iya samu a rediyo ba."

Koyaya dai, akwai kyakkyawan fata ga rediyo da makomarsa a matsayin babbar hanyar yada bayanai.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us