Afirka
1 minti karatu
Mutane da dama sun mutu a DRC sakamakon tashin bama-bamai yayin wani gangami na M23/AFC
Wasu fashe-fashe sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Kongo a lokacin gangamin 'yan tawayen M23/AFC.
Mutane da dama sun mutu a DRC sakamakon tashin bama-bamai yayin wani gangami na M23/AFC
Rikicin da aka shafe lokaci ana yi a gabashin Congo ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 7,000 a bana. Hoto (Getty Images)
vor 12 Stunden

Mutane da dama ne suka mutu wasu kuma suka jikkata sakamakon tashin bama-bamai a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a ranar Alhamis, yayin da ungiyoyin 'yan tawaye na M23/AFC ke wani ganganmi, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

Jagoran shirya gwangamin na ƙungiyoyin AFC/M23, Corneille Nangaa na dab da kammala taron a Bukavu a lokacin da bama-baman suka tashi, kamar yadda kafar yaɗa labaran intanet ta Congo Actualite ta rawaito, tana mai ambato shaidu.

Ƙungiyar M23 ta zafafa samin iko da kan iyaka a gabashin Congo tun watan Disamban da ya wuce, inda a baya bayan nan ta ƙwace manyan biranen gundumomin Goma da Bukavu.

Rikicin da aka shafe lokaci ana yi a gabashin Congo ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 7,000 a bana, a cewar Firaministan Congo Judith Suminwa Tuluka.

DR Congo tana zargin Rwanda da mara wa ƙungiyoyin 'yan tawaye baya, kuma ƙasashen da suka haɗa da Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Kigali takunkumai kan zarginta da goyon bayan 'yan tawayen da ake yi.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us