Nijeriya
2 minti karatu
NSCDC ta kama jarkokiN fetur 1,571 da ake zargin za a kai wa 'yan bindiga a jihar Zamfara
Biyu daga cikin waɗanda ake zargi, ma'aikatan da ke sayar da mai ne a wani gidan mai sai kuma sauran biyun da aka kama su a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Tsafe na jihar.
NSCDC ta kama jarkokiN fetur 1,571 da ake zargin za a kai wa 'yan bindiga a jihar Zamfara
NSCDC ta kama jarkunan fetur 1,571 da ake zargin za a kai wa 'yan bindiga a jihar Zamfara
il y a 13 heures

Hukumar tsaro ta farin kaya ta NSCDC reshen jihar Zamfara ta kama lita 1,571 ta man fetur da aka yi fasa ƙwaurinsu kana ake zargin za a kai su wuraren 'yan bindiga a jihar.

A yayin zantawarsa da manema labarai a madadin kwamandan NSCDC na jihar, jami'in hulɗa da jama'a rundunar Sani Mustapha ya bayyana cewa an kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata laifin a wurare biyu daban-daban.

Biyu daga cikin wadanda ake zargi, ma'aikatan da ke sayar da mai ne a wani gidan mai, sai kuma sauran biyun an kama su a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Tsafe na jihar.

A cewar Muhammad, baya ga kai fetur ɗin zuwa wajen da ba a amince da shi ba, mutanen da ake zargi sun kuma saɓa Dokar da Gwamna ya sanya wa hannu, wacce ta haramta sayar da albarkatun man fetur a jarka a cikin jihar Zamfara.

Ya bayyana cewa an kama biyu daga mutanen da ake zargi ne a Birnin Magaji da lita 1,296 ta fetur, yayin da aka kama sauran biyun a Tsafe da lita 275.

“A yau mun gabatar muku da mutane hudu da ake zargi da ta'ammali da man fetur mai yawa ba bisa ƙa'ida ba, inda suka saɓa wa Dokokin Ƙasa da na Jiha waɗanda suka hana sayar mai a jarkoki," a cewarsa.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us