Ko me ya sa wasu shahararrun ’yan wasa suke kasa yin katabus bayan sun koma Real Madrid?
Wasanni
4 minti karatu
Ko me ya sa wasu shahararrun ’yan wasa suke kasa yin katabus bayan sun koma Real Madrid?Real Madrid wacce ta lashe Kofin Zakarun Turai har sau 15 a tarihi dai kungiya ce da ’yan wasa da dama suke son zuwa su taka leda.
#NLA12 : Kaɗaita: Liga: Shirin kunna da kaamawa na kungiyar Real Madrid a gaban wasa da Girona
22. Januar 2025

Real Madrid wacce ta lashe Kofin Zakarun Turai har sau 15 a tarihi dai kungiya ce da ’yan wasa da dama suke son zuwa su taka leda.

Sannan ita kanta kungiyar tana kashe makudan kudaden wajen sayo ’yan wasa da suka shahara wanda a wasu lokuta ma su ne suka fi tsada a zamanin.


Sai dai kuma akan samu daga cikin irin wadannan yan wasa, sun kasa kawo bantensu bayan shigar su ƙungiyar, duk da makudan kudin da aka kashe musu, da kurarin kwarewarsu a baya.


Sai ka ga kamar ba su ne ’yan wasan da suka yi fice wajen murza leda da kuma burge ’yan kallo a kungiyar da suka baro ba.


Wannan ya sa wasu sun fara canfa Real Madrid, har suna cewa tana neman zama tamkar wata makabarta ta fitattun ’yan wasa.


Bari mu fara da Kylian Mbappé wanda ya koma Real Madrid daga PSG a watan Yunin bana wanda hakan abu ne da ya yi wa kungiyar da dan wasan, har ma da masoyansu dadi sosai.


Sai dai watanni bayan zuwansa Madrid, kyaftin din kasar Faransar ya gaza ba mara da kunya saboda kawo yanzu ya ci kwallaye tara kacal ne bayan ya buga wasanni 17 a kungiyar. Mbappé ya ci bugun fanareti uku ne cikin biyar din da ya dauka, wanda hakan ya sa ya zama shi ne dan wasan La Liga da ya fi barar da fanareti a kakar bana a halin yanzu.


A irin wannan lokaci san da yake wasa a PSG, dan kwallon ya taba cin kwallaye 17 a wasanni 13 da ya buga a tsohuwar kungiyar tasa.


Sannan wani dan wasa wanda shi ma ya kasa yin katabus a Madrid shi ne tsohon kyaftin din Wales a Burtaniya, wato Gareth Bale, wanda ya koma Real Madrid din daga Tottenham a shekarar 2013, wanda a lokacin dan kwallon ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi tsadar sayowa a duniya.


Shahararriyar jaridar wasannin nan ta kasar Sifaniya Marca ta taba siffanta Bale da wanda bai san yadda ake buga kwallon ba. Kuma ta ce ya san dai yadda ake yin gudu.


Wani karin misalin da ke nuna gazawar taurarin kwallo da ke komawa Madrid, shi ne tsohon dan wasan Belgium Eden Hazard, wanda ya shahara sosai lokacin da yake wasa a Chelsea a tsakanin 2012 zuwa 2019, inda ya ci kwallaye 85 a wasanni 245.


Amma kuma daga lokacin da ya koma Real Madrid a 2019, sai labari ya canja saboda kwallaye 4 kacal ya ci bayan ya yi wasanni 54. Ko da yake shi wannan dan wasa rashin nasararsa a Madrid na da alaka da raunin da ya ji da kuma doguwar jinyar da ya yi ta yi.


Wani dan jarida kuma masanin harkokin wasanni Mansur Abubakar ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa yana ganin babban abin da ya sa ake ganin kamar tauraruwar wasu ’yan wasa tana dusashewa bayan zuwan su Madrid bai wuce dogon burin da ake sanya wa ’yan wasan ba.


Ya ce Madrid ce babbar kungiyar kwallon kafa a duniya saboda haka duk inda dan wasa ya bari ya taho kungiyar, to duk kokarinsa wasu za su iya ganin kamar ya gaza.
Sannan masanin wasannin ya ce wasu daga cikin zakakuran ’yan wasan da suka koma Madrid kamar Mbappé suna bukatar lokaci kafin su saba da wasa a can.


 Ya bayar da misalin Cristiano Ronaldo wanda ya ce hatta shi ma bayan da ya koma Madrid daga Manchester United a shekarar 2009 ba daga zuwan sa ne tauraruwar ta fara haskawa ba a kungiyar. Ya ce sai da aka dan dauki wani lokaci.


Malam Mansur ya ce Mbappé ya fi iya buga lamba 11 amma kuma a Madrid yanzu Vinicius ne yake buga wannan lamba. Ya ce kuma yanzu yana da wuya a karbe buga lamba 11 daga hannun Vinicius a mika wa Mbappé saboda Vini ya fi shi kokari a wajen.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us