Türkiye
5 minti karatu
Daliban Syria a Turkiyya: Gada tsakanin Ankara da Damascus
Dalibai 'yan kasar Syria da ke karatu a jami'o'in Turkyya na zama manyan ginshikan samun karfin Turkiyya, suna kyautata makomar kasashen biyu a nan gaba.
Daliban Syria a Turkiyya: Gada tsakanin Ankara da Damascus
Syrian students in Turkey
27 Φεβρουάριος 2025

A manyan dakunan karatu na jami'o'in Turkiyya, cikin sirri wani al'amari na diflomasiyya na faruwa. Daliban kasashen waje da ke karatu a kasar sun karu ninki shida sama da yadda suke shekaru goma da suka wuce.

Daga cikin daliban kasashen waje 336,000 da ke karatu a Turkiyya, sama da 60,000 'yan kasar Syria ne, wanda ya sanya suka fi duk 'yan sauran kasashe dalibai yawa a kasar. Wannan na bayyana samun ninki 30 tun daga 2013 zuwa yau, inda daliban Syria suka zama daya cikin duk daliban kasashen waje biyar a Turkiyya.

Wadannan matasan masu ilmi ba iya zuba jai a bangaren ilimi kawai suke wakilta ba - sun zama wata gada tsakanin Ankara da Damascus bayan yakin kasar, wanda ke kyautata makomar kasashen biyu da ma ba a samun su a ajujuwan makaranta.

Nadin sabon ministan harkokin wajen Syria, Assad Hassan al Shaibani - wanda ya kammala karatu a jami'ar Istanbul Sabahattin - na bayyana wannan sauyi mai ma'ana.

Shaibani, wanda ke ci gaba da karatun digirgir a wannan jami'a, ya yi rubutun digirinsa na biyu manufofin Turkiyya a Syria, wanda ke bayyana hazakar siyasa da ake da ita.

Ba shi kadai ba ne, sabon gwamnan Aleppo, Azzam al-Gharib, shi ma tsohon dalibin sashen nazarn Musulunci na jami'ar Bingol ne da ke gabashin Turkiyya.

Wadannan dalibai da suka gama jami'a, na taka rawa a fagen siyasar Syria, sun zama abinda malamin jami'a a Amurka, Norman Kiell a 1951 ya kira da sunan "jakadu ba a hukumance ba".

A yayin da 'yan Syria da dama ke koma wa gida, da yawa za su taso su hau manyan mukamai, kuma ba ilimi kawai za su dakko daga Turkiyya su kai kasar ba, har ma da kusanci da fahimtar Turkiyya da ma fannoni masu kyau.

Sauran adadi mai yawa na dalibai ya fito ne daga kasashen Azerbaijan, Iran, Turkmenistan, da Iraki, wanda ke bayyana zuzzurfar alakar ilimi ta Turkiyya a yankin.

Daga dalibai zuwa 'yan kasuwa, da manyan masana

Baya ga siyasa, wadannan dalibai na na kawo habakar raya al'adu da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Hukumar Tsare-Tsare ta Istanbul (IPA) ta ce daliban kasashen waje na bayar da gudunmowar kusan dala biliyan 2.9 ga tattalin arzkin Turkiyya kowacce shekara, inda 'yan Syria ke kawo kimanin dala miliyan 522.

A shekarar da ta gabata, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wajen wani taro a Jami'ar Marmara da ke Istanbul ya bayyana irin muhimmancin da daduwar daliban kasashen waje ke da shi a Turkiyya, kuma a matsayin masu habaka tattaln arziki da zama gada tsakanin kasar da duniya. Ya yi karin haske da cewa kashi 95 na daliban na daukar nauyin kan su, gaskiyar da ke bayyana Turkiyya ta zama babbar cibiyar ilimi a duniya.

Kara yawan jami'o'i daga guda 76 a 2002 zuwa 208 a yanzu da dama mai gwabi da YTB ke bayarwa sun sanya Turkiyya zama kasa ta bakwai a duniya da aka fi zuwa karatu daga ketare, bayan Amurka, Canada, Birtaniya, Australia, Faransa da Jamus.

Wanzuwar kungiyoyin tsaffin daliban kasashen waje na kara karfafa alakar kasuwanci, inda sabon su da kasuwannin Turkiyya da ayyukan kasuwanci, sun habaka alakar kasuwanci da kasashensu bayan sun koma gida.

Ta hanyoyi da dama, an saita su su zama "jakadun kasuwanci' ga Turkiyya a zamanin da ake sake gina Syria.

Fagen ilimi ma na sauya salo.

Kasancewar sama da dalibai 'yan kasar Syria 60,000 ya habaka tsarin ilimi mai zurfi a Turkiyya, yana kara samar da yanayin koyo da koyarwa na kasa da kasa.

A yayin da wadannan dalibai da suka gaba jami'a suke rayuwa a Syria, za su kawo damar musayar ilimi, bincike da hadin kai, da zama kyakkyawar makomar diflomasiyya ga kasashen biyu.

Domin cimma wannan buri dari bisa dari, turkiyya na iya samar da "Dabarun ayyuka da 'yan kasar Syria da suka kammala karatu".

Duba ga wannan, ya kamata Turkiyya ta dauki wani mataki na musamman - wanda za ta ci ribar daliban kasashen waje da suka gama karatu, kamar dai yadda Amurka da Birtaniya suka yi.

A yanzu haka akwai wasu mutane 54 da suka yi karatu a Amurka kuma shugabancn kasashensu. Haka ma Birtaniya, inda a kasashe 53 ake da akalla babban jagora guda daya.

Turkiyya na da tsari abin koyi.

Domin karfafa alaka da dangantaka tsakanin Turkiyya da daliban kasashen waje da suka kammala karatu a kasar, ya zama lallai Turkiyya ya karfafa alaka da tsaffin dalibai don samun babbar alaka da su. Wannan zai tabbatar sadarwar kai tsaye da su, ba tare da wani na tsakiya ba.

Ta hanyar zuba jari kan wadannan dalibai, ba ilmantar da al'umma Turkiyya ke yi kawai ba - tana assasa harsashin hadin kai madauwami da kasashensu ne.

Dalibai 'yan kasar Syria da ke karatu a jami'o'in Turkyya na zama manyan ginshikan samun karfin Turkiyya, suna kyautata makomar kasashen biyu a nan gaba.

Marubucin, Farfesa Faruk Tasci, shi ne daraktan Cibiyar Daliban Kasashen Waje a Jami'ar Istanbul.

Togaciya: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba lallai ba ne ya zo daidai da ra'ayi,hange da manufofin editan TRT Afrika.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us