Wasanni
2 minti karatu
Messi zai dawo Barcelona, amma Neymar ba zai komo ba: Shugaban La Liga
Shugaban La Liga, Javier Tebas ya bayyana tunaninsa kan yiwuwar dawowar gwarazan tsofaffin 'yan wasan Barcelona, Lionel Messi da Neymar Jr.
Messi zai dawo Barcelona, amma Neymar ba zai komo ba: Shugaban La Liga
Shugaban La Liga, Javier Tebas ya ce Barcelona na alfahari da sunan Messi. / Hoto: Reuters
8 saat əvvəl

Yayin da aka daɗe ana raɗe-raɗin gwarzon ɗan wasan Barcelona, Lionel Messi zai koma ƙungiya, rahotanni sun ambato shugaban La Liga yana tabbatar da yiwuwar hakan.

Shugaban La Ligar, Javier Tebas ya bayyana tunaninsa kan dawowar gwarazan tsofaffin 'yan wasan biyu zuwa Barcelona, wato Messi da Neymar, inda ya ce yana ganin tabbas hakan zai faru.

"Ina ganin Messi na son ya dawo Barcelona. Ya kwashe tsawon shekaru a can. Ƙwarai na tabbata Messi zai dawo, wataƙila a matsayin ɗan wasa, amma na san zai iya komowa a wani matsayin daban... Sunansa da sunan Barcelona abu guda ne. Yana ƙaunar kulob ɗin", cewar Javier Tebas.

Da yake magana kan Neymar kuwa, ya ce "Neymar wani zancen ake yi. Ba na jin zai dawo Barcelona. Ina da tabbacin hakan."

Wasa tare

Lionel Messi da Neymar sun kwashe kaka huɗu tare a Barcelona, kafin Neymar ya koma Paris Saint-Germain a 2017. Shekaru huɗu bayan nan, Messi ya bi Neymar zuwa PSG, bayan kwantiraginsa a Barca ta ƙare.

A 2023, duka su biyun sun raba gari da PSG, inda Messi ya tafi Amurka ya shiga ƙungiyar Inter Miami da David Beckham ya mallaka.

Shi kuwa Neymar ya tafi ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya. Amma a Janairun nan ya baro can ya koma ƙungiyar da ya fara wasa lokacin da yana matashi, wato Santos ta Brazil.

Ana ƙarfafa tunanin Neymar zai koma Turai a bazara mai kamawa, inda Barcelona ke cikin jerin ƙungiyoyin da zai iya komawa. Nan gaba a shekarar nan, ana sa ran shi ma Messi zai koma Sifaniya a matsayin wucin-gadi.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us