Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta yi kira a ranar Laraba kan a dinga yanke hukunci daurin rai da rai da kuma hukuncin kisa ga wadanda aka kama suna sayar da jabun magunguna.
NAFDAC ta bayyana cewa NIjeriya ta kwashe shekaru tana fama da matsalar yaduwar jabun magunguna, musamman maganin zazzabin cizon sauro da maganin rage raɗaɗi da kuma maganin kashe ƙwayoyin cuta.
Shugabar hukumar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa, a wannan sabon samame wanda jami’an tsaro suka taimaka a yin sa, an kama jabun magunguna masu yawa da kuma wadanda ba su dace ba, da magungunan da hukumar USAID ke bayarwa kyauta na HIV, da magungunan kashe kwayoyin cuta da kuma kwaroron roba da lokacin amfaninsu ya ƙare.
An ƙwace ɗumbin magunguna irin su Tafrodol, wani magani da aka haramta a Nijeriya, da allurar oxytocin da ake amfani da su a lokacin haihuwa.
'An jibe wasu a banɗaki'
“An gano wadannan kayayyakin ne a cikin bandaki, da karkashin ƙafar bene da kuma saman rufin daƙuna a cikin tsananin zafi, ba tare da la’akari da bukatar ajiye su a cikin sanyi ba,” in ji Adeyeye a cikin wata sanarwa.
Adeyeye ta bukaci ‘yan majalisa da su hanzarta bin dokar da aka yi wa kwaskwarima kan kwayoyi da lafiya “don saka hukuncin daurin rai-da-rai (da) hukuncin kisa kan laifukan da aka aikata a karkashin wadannan dokokin.
Sauran laifufukan da ake yankewa hukuncin kisa a Nijeriya sun hada da fashi da makami da kisan kai da cin amanar kasa da kuma ta’addanci, amma tun daga shekarar 2016 aka mayar da akasarin hukuncin zuwa zaman gidan yari.
A baya dai hukumar da ke yaki da muggan kwayoyi ta kai samame a kasuwanni amma aikin na baya bayan nan wanda aka fara tun a ranar 9 ga watan Fabrairu shi ne mafi girma har yanzu, inda ya auka a babban birnin kasuwanci na Legas da kuma jihohin Anambra da Abia na kudu maso gabashin kasar.
A Nijeriya, kasa mai mutum sama da miliyan 200, ana sayar da jabun magunguna da yawa a kasuwanni barkatai ba tare da nuna takardar magani daga likita ba.