Hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta yi hasashen cewa za a fara damuna da sauri a wasu sassan ƙasar.
A wani cikakken rahoton da ta fitar kan hasashen yanayi na shekarar 2025, hukumar ta yi hasashen cewa za a samu jinkiri kafin damuna ta kankama a yawancin jihohin arewacin Nijeriya.
Jihohin da ake tsammanin jinkiri kafin damuna ta kankama sun haɗa da Sokoto da Zamafara da Katsina da Jigawa da Filato da Bauchi da Gombe da sassan Jihar Kebbi da Neja da Kaduna da Adamawa da Nasarawa da Kwara da Oyo da Ekiti.
Rahoton ya yi hasashen cewa damuna za ta fara kankama da wuri a jihar Bayelsa da Delta da Rivers da sassan jihohin Legas da Ondo da Edo da Enugu da Anambra da Ebonyi da kuma jihar Oyo.
Yadda damuna za ta kankama
Hukumar ta yi hasashen cewa damuna za ta kankama ne daga ranar 28 ga watan Fabrairu a jihohin Delta da Bayelsa da Rivers da kuma Akwa Ibom.
A jihar Lagos da kuma wasu sassan jihohin Ogun da Osun da Ondo da Edo da Anambra da Imo da Cross River kuwa ana hasashen za a fara damunan ne daga ranar 15 ga watan maris.
Sai ranar 30 ga watan Maris ne ake sa ran za fara damuna a wasu sassan jihohin Ogun da Oyo da osun da Ekiti da Edo da Anambara da Enugu da Ebonyi.
A wasu sassan jihohin Oyo da Kwara Neja da Ekiti da Enugu da Benue da Taraba da Nasarawa da Filato da Kaduna da Abuja kuwa zai kai ranar 29 ga watan Afrilu kafin a fara damuna.
Har ila yau hasashen na hukumar NiMET ya nuna cewa za a kai ranar 14 ga watan Mayu kafin a samu damuna a wasu sassan jihohin Neja da Kaduna, Nasarawa da Abuja, da Adamawa da Gombe da Bauchi da Kano da Kebbi da Zamfara.
A wasu sassan Zamfara da Sokoto da Kebbi da Kaduna da Katsina da Jigawa da Abuchi da Gombe da Yobe da Barno kuwa damuna za ta kai ranar 29 ga watan Mayu kafin ta fara.
Sai kuma wasu sassan jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Jigawa da Yobe da Borno kuma inda za ta kai ranar 13 ga watan Yuni kafin damuna ta kankama.
Ƙarshen damuna
Hukumar ta NiMET ta yi hasashen cewa damuna za ta ƙare da wuri a jihohin Gombe da Kano da sassan jihohin Bauchi da Kaduna da Kogi da Jigawa da Zamfara da Filato da Katsina da Zamfara Neja da Kwara da Ekiti da Edo da Abuja
Wasu jihohi irin su Legas da kuma sassan jihohi irin su Nasarawa da Benue da Taraba da Filato da Cross River, Ebonyi da Enugu da Anambra da Delata da Akwa Ibom kuwa ana hasashen damuna ba za ta ƙare da wuri ba.
Ɗaukewar ruwa
Har ila yau NiMET ta yi hasashen cewa ruwa zai ɗauke sosai tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta a sassan jihohin Sokoto Zamfara da Katsina da Kano da Kaduna da Jigawa da Bauchi da Gombe da Neja da Kwara da Oyo.
Kazalika hasashen ya ce za ruwa zai ɗauke sosai a jihar Oyo tsakanin watan Afrilu zuwa watan Yuni.
Barazanar ɗaukewar ruwa a ƙananan hukumomi
NiMET ta ce ƙananan hukumomi irin su Abadam da Bama da Mobbar da Kukawa da Guzamala da Gubio da Nganzai da Monguno da Marte da Ngala da Bama da Gwoza da Kaga da Mafa da Magumeri a jihar Borno za su fuskanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta.
A jihar Yobe kuwa ƙananan hukumomi irin su Barde da Bursari da Damaturu da Fika da Potiskum da Geidam da Machina da Nguru da Karasuwa da Yunusari da Yusufari da Jakusko da Tarmuwa su ma na fuskantar barazanar ɗaukewar ruwa fiye da kwana 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta, in ji rahoton.
Kazalika rahoton ya ce a jihar Katsina ƙananan hukumomi irin su Baure da Batsari da Bindawa da Batagarawa da Daura da Charanchi da Kankia da Jibia da Rimi da Mani da Mashi da Mai’Adua da Matazu da Katsina da Dutsi da Sandamu da Ingawa da Zango za su fuskanci ɗaukewar ruwa na sama da kwani 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta, in ji NiMET.
Ƙananan hukumomin Babura da Birniwa da Gwiwa da Garki da Roni da Kazaure da Gumel da Guri da Yankwashi da Kirkasama da Maigatari da Kaugama da Sule-Tankarkar da Malam Madori a jihar Jigawa kuwa su ma za su faukanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanani 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta.
A jihar Bauchi kuwa ƙananan hukumomin Damban da Darazo da Gamawa da Giade da Itas/Gadau da Jama'are da Katagum da Misau da Ningi da Shira da Warji da Zaki ne za su faukanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni da Agusta.
Ƙananan hukumomin jihar Yobe da za su fsukanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zuwa Agusta sun haɗa da Barde da Bursari da Geidam da Machina da Nguru, Karasuwa da Yunusari da Yusufari da Jakusko da kumaTarmuwa.
A jihar Kebbi kuwa ƙananan hukumomin da za su fuskanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanani 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta kuwa sun haɗa da Arewa Dandi da Aleiro da Kalgo da Bunza da Birnin Kebbi da Argungu da Augie da Jega da Maiyana.
Ƙananan hukumomin Bichi da Dambata da Makoda da Tsanyawa da Kunchi da Bagwai, Gwarzo da Tofa a jihar Kano suna cikin ƙananan hukumomin za su fuskanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta.
Idan kuma aka leƙa jihar Zamfara kuwa, hasashen NiMET ɗin ya ce ƙananan hukumomin Anka da Bakura da Birnin Magaji da Bukkuyum da Bungudu da Gummi da Kaura Namoda da Shinkafi da Talata Mafara da Tsafe ne za su fuskanci ɗaukewar ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zwa watan Agusta.
A jihar Sokoto kuma ƙananan hukumomin da za a samu ɗaukewar ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta sun haɗa da Binji da Bodinga da Dange Shuni da Gada da Gwadabawa da Illela da Isa da Rabah da Shagari da Silame da Tambuwal da Yabo.
Ƙananan hukumomin Nafada da Yamaltu-Deba da Dukku da kuma Funakaye ne hasashen NiMET ke ganin za a ɗauke ruwa na sama da kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta.
Sai kuma ƙananan hukumomin Langtang North da Kanke a jihar Filato da hasashen NiMET ke cewa za su fuskanci ɗaukewar ruwa da ya zarce na kwanaki 21 tsakanin watan Yuni zuwa watan Agusta.