Siyasa
2 minti karatu
Nijar na da niyyar sa wa kafafen sada zumunta linzami: Minista
Sidi Mohamed Raliou ya bayyana cewa "nan ba da jimawa ba za a bayar da shawara game da tsayayyar mafita domin tabbatar da tsari mai tsabta wajen ƙayyade amfani da kafafen sada zumunta a Nijar."
Nijar na da niyyar sa wa kafafen sada zumunta linzami: Minista
Ministan ya ce wasu na amfani da shafukan sada zumunta wajen yi wa gwamnatoci zagon ƙasa
8 часов назад

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet na Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou, ya ce ƙasar tana da niyyar saka ƙa’idodji na amfani da kafofin sada zumunta.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar ya ruwaito cewa ministan ya faɗi hakan ne a lokacin da yake bayani a gidan talabijin na ƙasar game da ayyukan ma’aikatarsa a shekarar 2024.

Minista Sidi Mohamed Raliou ya bayyana cewa shi da abokan aikinsa suna tunanin hanyar da ta fi dacewa wajen ƙayyade amfani da kafafen sada zumunta musamman ga waɗanda ke amfani da su cikin jama’a da yawa maimakon mutane ƙadan.

"A lokacin da aka kafa guruf a Whatsapp, wannan wata ƙungiya ce," a cewar ministan, yana mai jaddada cewa ƙayyade amfani da kafafen zai zama wajibi ne idan ‘guruf’ ya haɓaka.

"Idan mai gida ne da matarsa, wannan babu laifi game da shi. Amma idan ya kasance wata tarayyar mutane, wata ƙungiyar mai zaman kanta ko ta siyasa mai mutane 50 ko 100, wannan ya kai wani mataki na daban " in ji shi, yana mai nuni da cewa yana kan tuntuɓar abokanan aikinsa daga sauran ƙasashen Afirka masu ƙayyade amfani da kafafen sada zumunta a rayuwar yau da kullum.

 

"Wannan tsarin yana kasancewa dole a yi shi ne domin kafafen sun zama ababe masu amfani ga wasu da kuma hanyar yi wa gwamnatoti zagon ƙasa ga wasu " in ji ministan sadarwar.

 

Sidi Mohamed Raliou ya bayyana cewa "nan ba da jimawa ba za a ba da shawara game da tsayayyar mafita domin tabbatar da tsari mai tsabta wajen ƙayyade amfani da kafafen sada zumunta a Nijar ".

"Za mu yi nazari tare, za mu samar da takardu tare da gwamnati domin ganin yadda za mu ƙayyade amfani da waɗannan kafafen sada zumuntan " a cewarsa.

TUSHEN:Public domain
Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us