Afirka
1 minti karatu
Adadin waɗanda suka rasu a hatsarin jirgin sojin Sudan ya ƙaru zuwa 46
Sojojin Sudan a ranar Talata sun sanar da cewa wani jirgi ya faɗi a lokacin da ya tashi a sansanin sojin Wadi Seidna da ke arewacin Omdurman a Jihar Khartoum, wanda ya jawo sojoji da fararen hula suka rasu.
Adadin waɗanda suka rasu a hatsarin jirgin sojin Sudan ya ƙaru zuwa 46
Babu cikakken bayani zuwa yanzu game da faɗuwar jirgin
February 27, 2025

Adadin waɗanda suka rasu sakamakon hatsarin jirgin soji na Sudan ya ƙaru zuwa 46, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Lamarin ya faru ne a kusa da Khartoum babban birnin ƙasar a ranar Talata inda tun da farko aka ruwaito cewa mutum goma ne suka rasu.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan faɗuwar jirgin, amma kamfanin dillancin labarai na Sudan SUNA ya ce akwai mutum goma waɗanda suka jikkata.

Sojojin Sudan a ranar Talata sun sanar da cewa wani jirgi ya faɗi a lokacin da ya tashi a sansanin sojin Wadi Seidna da ke arewacin Omdurman a Jihar Khartoum, wanda ya jawo sojoji da fararen hula suka rasu.

Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙi tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF inda fiye da mutum 20,000 suka rasu, mutum miliyan 14 kuma suka jikkata, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana. Wani bincike da jami’o’i a Amurka ya suka yi ya bayyana cewa adadin waɗanda suka rasu ya kai 130,000.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us