Nijeriya
2 minti karatu
Shugaban Nijeriya Tinubu ya sa hannu kan kasafin kudin 2025 na Naira Tiriliyan 54.99
A ranar 13 ga watan Fabrairu ne Majalisar Dokokin Ƙasar ta amince da kudirin bayan yi masa wasu gyare-gyare.
Shugaban Nijeriya Tinubu ya sa hannu kan kasafin kudin 2025 na Naira Tiriliyan 54.99
Nigeria budget 2025
5 orë më parë

Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin shekarar 2025 na Naira Tiriliyan 54.99 ya zama doka.

Kasafin kudin 2025 ya fi na shekarar 2024 da kashi 99.96% na naira tiriliyan 27.5.

Tinubu ya sanya hannu a ofishin sa da ke fadar gwamnatin tarayya a Abuja ranar Juma’a. An kara kudirin ne daga kididdigar farko ta naira tiriliyan 49.7 da shugaban Nijeriya ya gabatar.

A ranar 13 ga watan Fabrairu ne Majalisar Dokokin Ƙasar ta amince da kudirin bayan yi masa wasu gyare-gyare.

Takaddar kasafin kudin ta nuna cewa ya hada da jimillar kashe tiriliyan ₦54.99 da kuma fitar da naira tiriliyan 3.65 bisa doka. Kudaden da ake kashewa (ba na bashi) sun kai tiriliyan ₦13.64.

Kudaden da za a kashe na manyan ayyuka sun kai naira tiriliyan 23.96, za a kashe naira tiriliyan 14.32 a biyan basussuka, yayin da aka sanya gibin da za a samu na ma’aunin tattalin arziki GDP a kashi 1.52%.

A farkon watan ne Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dokokin Kasar saƙo game da gyara kasafin kudin 2025.

A cewar Shugaba Tinubu, ƙarin kudin da aka samu ya kai tiriliyan 1.4 na karin kudaden shiga daga hukumar tara haraji ta kasa FIRS, da tiriliyan 1.2 daga hukumar kwastam ta Nijeriya (NCS), da kuma tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka samu.

Ya gabatar da kasafin kudin farko ga majalisar kasa a ranar 18 ga Disamba, 2025.

"Abin farin ciki ne da nake gabatar da kasafin kudin 2025 na iajeriya mai taken, 'The Restoration Budget' tabbatar da zaman lafiya, da wadata," ga wannan babban taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa, in ji Tinubu.

"Kudirin kasafin kudin 2025 na neman dawo da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki, inganta yanayin kasuwanci, samar da ci gaba mai hade da juna, ayyukan yi da rage talauci, inganta rarraba kudaden shiga da kuma bunkasa jarin bil'adama," in ji Tinubu.

 

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us