Wani jirgin sojin Sudan ya yi hatsari a ranar Talata a kusa da Khartoum babban birnin ƙasar, inda sojoji da farar hula da dama suka rasu, kamar yadda sojojin ƙasar suka bayyana, inda wasu masu goyon bayan dimokuraɗiyya suka ce aƙalla mutum goma ne suka rasu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Talata, rundunar sojin Sudan da ke yaki da dakarun Rapid Support Forces (RSF) tun a watan Afrilun 2023, ta ce jirgin ya fado ne a lokacin tashinsa a wani sansanin sojin sama, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an soji da fararen hula.
Sanarwar ta kara da cewa, "An kai waɗanda suka jikkata asibiti, kuma jami'an kashe gobara sun yi nasarar shawo kan gobarar a wurin da hadarin ya afku."
Tun da farko wata majiyar soji ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, matsala jirgin ya samu shi ya sa ya faɗo bayan ya tashi.
Lalata gidaje da dama
Jirgin ya yi hatsari ne a kusa da sansanin sojin sama na Seidna — ɗaya daga cikin sansanonin soji mafi girma a Omdurman.
Wata ƙungiya ta Karari Resistance Committee, wadda ƙungiya ce ta sa kai da bayar da agaji a faɗin Sudan, ta bayar da rahoton cewa an kawo gawawwaki 10 da kuma mutane da dama waɗanda suka jikkata asibitin Al-Nao da ke Omdurman.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa jirgin da ya faɗo ya lalata gidaje da dama.
Mazauna kudancin Omdurman sun ce sun ji wata ƙara a lokacin da jirgin ya yi hatsarin, wanda hakan ya jawo katsewar wutar lantarki a unguwanni da dama.
Iƙirarin RSF na harbo jirgin soji
Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa jirgin ya nufi kudi bayan ya tashi inda
Wannan lamarin na zuwa ne kwana guda bayan rundunar RSF ta Sudan ya yi iƙirarin cewa ta kakkaɓo wani jirgin yaƙi a Nyala babban birnin Kudancin Darfur.
A wata sanarwa da ta aika wa kafafen watsa labarai, RSF ɗin ta ce ta harbo wani jirgin ƙirar Rasha a safiyar Litinin, inda ta ce ta harbo jirgin da mutanen da ke ciki.
Wannan ƙaruwar rikicin na zuwa ne bayan sojojin ƙasar sun ƙara matsawa tsakiyar Sudan da kuma Khartoum babban birnin na Sudan a fagagen daga daban-daban da take fafatawa da RSF.