Afirka
2 minti karatu
Nijar ta samu CFA biliyan 204 a matsayin kuɗin shiga daga man fetur a 2024 — Minista
Ministan Man Fetur na Jamhuriyar Nijar Dakta Sahabi Oumarou ya ce kuɗin shigar da ƙasar ta samu daga fetur babban ci gaba ne a gare ta idan aka kwatanta da CFA biliyan 64.1 da ta samu a shekarar 2020.
Nijar ta samu CFA biliyan 204 a matsayin kuɗin shiga daga man fetur a 2024 — Minista
Nijar ta zama ƙasar da ke samar da mai a shekarar 2011 bayan gano mai a Goumeri da Sokor da Agadi da ke yankin Diffa. / Hoto: Reuters
26 de febrero de 2025

Jamhuriyar Nijar ta samu kuɗin shiga ta hanyar man fetur da suka kai CFA biliyan 204 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da CFA biliyan 64.1 da ƙasar ta samu a shekarar 2020.

Ministan man fetur na ƙasar Dakta Sahabi Oumarou ne ya bayyana haka a lokacin da ya tattauna da gidan talabijin na ƙasar.

Da yake magana kan gudummawar da man fetur ke bayarwa a kasafin kudin kasar musamman ma ga tattalin arzikin ƙasar, minista Sahabi Oumarou ya bayyana cewa man fetur ya kasance wani abu ne da ta dogara da musamman bayan abubuwan da suka faru a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Oumarou ya ƙara da cewa a “shekarar 2020, kashi 2.86 cikin 100 na kasafin kuɗin Nijar daga kuɗin shiga na man fetur ne, mun samu biliyan 64.1, a 2024 kuma muna samu biliyan 204 kuma abubuwa suna kyau”.

Ta ɓangaren tattalin arziki, ministan ya bayyana cewa ‘yan ƙasar da dama sun samu ayyukan yi a kamfanonin mai na ƙasar.

A kamfanin mai na CNPC, ‘yan Nijar 409 suka samu aiki kai tsaye a can, a kamfanin mai na SORAZ, ‘yan ƙasar ta Nijar 442 suka samu aiki, sannan kuma a WAPPCO, akwai ‘yan ƙasar 85 da suka samu aiki.

Tun bayan da sojojin ƙasar suka karɓi mulki a shekarar 2023, sun sha iƙirarin samun ci gaba a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar.

Ko a shekarar 2024 da ta gabata sai da gwamnatin Nijar da wani kamfanin ƙasar Canada, Zimar, suka sa hannu kan wata yarjejeniya domin gina sabuwar matatar mai a yankin Dosso da ke makwabtaka da Benin. Ana sa ran matatar man da za a gina za rinƙa tace ganga 100,000 a kullum.

Nijar ta zama ƙasar da ke samar da mai a shekarar 2011 bayan gano mai a Goumeri da Sokor da Agadi da ke yankin Diffa.

A Janairun 2012, Nijar ɗin ta ƙaddamar da matatar manta ta farko wadda ke da ƙarfin tace ganga 20,000 a duk rana a yankin Zinder.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us