Bikin bayar da kyautar Ballon d’Or ta bana ya daure kan magoya bayan Vinicius Junior da Real Madrid bayan an bayyana gwaninsu a matsayin wanda ya zo na biyu kuma aka bayyana dan wasan tsakiyar Manchester City ɗan asalin Sifaniya, Rodri a matsayin wanda ya lashe kyautar a bana.
Wakilan kungiyar Real Madrid da Vinicius ba su halarci bikin bayar da kyautukan ba wanda aka yi a birnin Paris a ranar Litinin, wanda hakan alama ce da take nuna cewa dan wasan da kungiyarsa sun ji kishin-kishin cewa ba shi ne za a bai wa kyautar ba wanda hakan ya sa ba su halarci taron ba.
Magoya bayan Madrid suna ganin a wannan shekara Vini ne ya fi kowane dan wasa cancantar lashe gasar ganin cewa shi ne ya taimaka wa kungiyarsa ta dauki Kofin La Liga da kuma Kofin Zakarun Turai a bara.
A daya bangaren Rodri ya taimaka wa kasarsa Sifaniya ta dauki Kofin Euro 2024 a watan Yulin bana da kuma taimaka wa Manchester City sake daukar Kofin Premier na Ingila da Uefa Super Cup da kuma Club World Cup.
Sai dai Vinicius ya yi amannar cewa rashin nasararsa tana da alaƙa da fafutukarsa kan yaki da wariyar launin fata a kwallon kafa a Sifaniya, kamar yadda wasu makusantan dan wasan suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X dan wasan ya ce: “Zan sake yin bajinta ninki 10 idan haka ake so na yi. Ba su shirya ba.”
Sakon nasa ya samu tsokaci fiye da 120,000 bayan wasu sa’o’i, inda wasu suke cewa ba a yi wa dan wasan adalci ba, don a fahimtarsu shi ne ya fi kowa cancantar ya lashe kyautar.
Cikin wadanda suka yi tsokaci a karkashin sakon dan wasan, wanda dan asalin kasar Brazil ne, har da Ministar da ke Kula da Daidaito ta Fuskantar Mutane Masu Mabambantar Launin Fata a kasar Brazil (wato Minister of Racial Equality) Anielle Franco wacce ita ma bakar fata ce. Ministar ta jinjinawa dan wasan. Kuma ta ce wariyar launin fata ba zai dakatar da mu ba. Mu ci gaba da kafa tarihi.
Sai dai wasu masana harkokin wasanni suna ganin batun cewa wariyar launin fata ne ya hana shahararren dan wasan cin kyautar Ballon d’Or zance ne kawai.
Wasu masana harkokin wasanni suna ganin cewa da a ce Brazil da Vinicius sun taka rawar gani a Gasar Copa America ta bana kuma a ce kasarsa ce ta lashe kofin, to babu wata tantama Vinicius ne zai lashe kyautar Ballon d’Or a bana. Amma idan za a tuna Uruguay ce ta cire Brazil daga gasar a matakin kwata-final a farkon watan Yuli. A fahimtar masanan wannan ne dalilin da ya sa bai samu kyautar ba. Masanan sun ce babu shakka Vini yana taka rawar gani a Madrid, amma kuma ba ya taka wata rawar gani a Brazil.
Sannan masanan suna ganin a fili take irin rawar da Rodri ya taka wajen taimaka wa kasarsa Sifaniya ta lashe Euro 2024 da kuma kungiyarsa Man City a kakar da ta gabata.
Ce-ce-ku-ce kan kyautar Ballon d’Or ba sabon abu ba ne, saboda idan za a tuna a shekarar da dan wasan bayan Italiya Fabio Cannavaro ya ci kyautar wato shekarar 2006, masoya kwallon kafa da dama suna ganin shahararren dan wasan Faransa Zinedine Zidane ya fi shi cancanta.
Kazalika a shekarar 2003 lokacin da galibin masoya kwallon kafa suke ganin babu wani da ya fi shahararren dan wasan gaban Arsenal Thierry Henry cancantar ya lashe kyautar, amma sai kawai aka ji an sanar da sunan dan wasan tsakiyar Juventus kuma dan kasar Czech, Pavel Nedved, a matsayin wanda ya lashe kyautar a shekarar.
Kamar yadda yanzu muke ganin kan batun Vinicius haka a wancan lokacin aka rika bijiro da dalilai iri-iri ciki har da zargin nuna wariyar launin fata da sauransu.
Wata mujallar kwallon kafa da ke kasar Faransa wadda ake kira France Football ce take shirya kyautar Ballon d’Or duk shekara, kimanin shekaru 70 kenan.
Kuma wasu ’yan jarida kan harkokin kwallon kafa daga kasashe 100 da ke cikin jadawalin hukumar Fifa ne suke kada kuri’arsu kan jerin ’yan wasan 30.
Kowane dan jarida yana zabar ’yan wasa 10 daga cikin 30 da a ganinsa su ne suka fi hazaka wadanda zai jera su a mataki daga na 10 zuwa na daya.
Rumbun Labarai