Daga Abdulwasiu Hassan
12 ga Yunin 1993, ba rana ce kawai da ke kan kalanda ba a Nijeriya. Rana ce da ta samu gurbin zama a ƙwaƙwalen 'yan ƙasar, duk afkuwar lamarin shekaru 30 da suka gabata.
Wannan rana ce da Nijeriya ta shaida ganin samun sauyin jagoranci zuwa dimokuradiyya da aka dade ana jira.
Miliyoyi sun jefa kuri'insu wanda abu ne na tarihin rayuwarsu. Amma sai al'amura suka juya, lamarin da ya faro da kyau sai ya koma rikicin da ya kai ga soke zaben gaba daya.
Matakin ba tsarin dimokuradiyya kawai ya kawo wa cikas ba, ya ma bar babban tabo a fagen siyasar Nijeriya. 12 ga Yuni ta zama alamar fata nagari da kalubalen da ke zuwa da sauyin siyasa.
A yayin da rushe zaben ya zama batu mai rikitarwa, fitar da littafin tarihin rayuwarsa da tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya yi a makon da ya gabata ya janyo waiwaye da tattauna yanayin siyasar da kasar ta samun kanta a ciki a wancan karon.
Babangida ya karbi laifin soke zaben, amma ya alakanta matakin ga wasu mutane da da shugaban sojojin kasa na wannan lokacin marigayi Janaral Sani Abacha ke jagoranta, yana mai cewa an soke zaben ba tare da saninsa ba. Daga baya Abacha ya zama shugaban Nijeriya.
"Eh, a yayin hargitsin da ya biyo bayan soke sakamakon zaben, ba a samu damar tattauna soke zaben da zai kai ga gudanar da sabon zabe," Babangida ya rubuta a sabon littafinsa, A Journey in Service.
"Amma soke zaben gaba daya ya zama wani bangare na zabi da yawa da ake da su. Amma a ce a yi sanarwa ba tare da izinina ba babban lamari ne mai ban tsoro... Na tuna sanda nake cewa 'Wadannan mugayen da ba sa son zaben nan sun ci karfina!'
"Daga baya na samu labarin wasu gungun mutane karkashin jagorancin Sani Abacha ne suka soke zaben.
Hargowar jiya
A karkashin tsohuwar gwamnatin Babangida, an gabatar wa 'yan Nijeriya zabi tsakanin Moshood Abiola na jam'iyyar SDP da Bashir Tofa na jam'iyyar NRC.
A yayin da sakamako ya fara nuna cewa Abiola na SDP ne ke kan gaba, sai Hukumar Zabe ta lokacin ta dakatar da sanarwar.
Kwanaki sha daya bayan hakan, an soke zaben, wanda aka bayyana a mai cike da adalci kuma mafi sahihanci a tarihin Nijeriya.
Wannan soke zabe da ba a yi tsammani ba ya janyo zanga-zanga da Allah wadai, wanda ya sanya Shugaba Babangida yin murabus tare da bai wa gwamnatin riƙo dama, wadda daga baya Janar Sani Abacha ya kifar da ita tare da hawa mulki, a lokacin yana muƙamin shugaban rundunar sojojin kasa na Nijeriya.
Har sai a shekarar 1999 ne aka dawo turba dimokuradiyya da ta dore a Nijeriya.
Marubuci dan Nijeriya Abubakar Adam Ibrahim, wanda littafinsa da ke tafe ya faro da 12 ga Ynin 1993, ya bayyana tasirin soke zaben.
"Miliyoyin 'yan Nijeriya sun sa rai kan zaben da cewa zai zama wata babbar gaba mai muhimmanci a tarihin kasar.
“Kusan shekaru goma sojoji suka dauka suna shake 'yan siyasa, sai suka ba su damar yin zabe na gaskiya babu maguɗi, sannan kuma suka soke zaben gaba daya, hakan ya zama babban ta'annati da sojoji suka yi wa 'yan Nijeriya," ya fada wa TRT Afrika.
Rikicin da ake ci gaba da yi
Idan Babangida ya sa ran maganarsa za ta kawo karshen zancen, martanin da aka mayar ga littafin tarihin rayuwarsa na nuni da wani abu daban.
Bayan wannan sanarwa, magoya bayan Janar Sani Abacha sun soki tsohon shugaban, suna zargin sa da ɗora laifi kan wani da ba ya nan ballantana ya kare kansa.
"Har bayan ka mutu, kai ne babban abokin gogayyar su," Gumsu Abacha, 'yar Sani Abacha ta rubuta a shafinta na sada zumunta.
Abubakar na daga cikin wadanda ke tantama kan ikirarin na Babangida.
"Kamar dai ana wasa da hankali ne, a gefe daya ya ce ya dauki alhakin duk abubuwan da suka faru, a lokaci guda kuma yana ɗora laifin soke zaben a kan wasu da ba sa nan don su kare kawunansu," ya fada wa TRT Afrika.
Ya yi amanna cewa kalaman Babangida da suka gabata sun saba wa wandanda yake yi a yanzu haka.
"Wannan babbar dama ce da ya rasa. Da tuni ya zama zakakurin dan Nijeriya da ya baiwa Nijeriya zabe na gaskiya amma ya yi asarar wannan. Yanzu yana kewar wannan dama, kawai shi ne magana ta kai tsaye."
Neman yadda za a kawo karshen batun
A lokacin mulkinsa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar da ranar 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya.
Amma duk da haka, wannan mataki bai warware wannan dadaddiyar matsala da ta dabaibaye lamarin na na 12 ga Yuni, kamar yadda littafin tarihin kansa da Babangida ya rubuta ya bayyana.
Masu nazari na muhawarar cewa ba za a manta da wannan matsala ba har sai an dabbaka dimokuradiyya mai inganci da za ta amfanar da mutane.
"Ba zai yiwu a yi nadamar wannan kuskure na dimokuradiyya yanzu ba saboda manyan wadanda suka taka rawa a batun sun mutu," in ji Abubakar.
Matashin marubucin na son a dinga gudanar da zabe mai inganci, ta yadda ba za a maimaita kura-kuran da aka yi a baya ba.
Yana kuma kallon 12 ga Yuni a matsayin wata tsatsuniya ta daukar darasi. "Wani abu da ba za mu so mu manta shi ba shi ne ranar da lamarin ya faru."