Gwamnan jihar Kano a arewacin Nijeriya ya sanar da dakatar da Shugaban Ma’akata Salisu Shehu ba tare da ɓata lokaci ba, kan zargin zaftare albashin ma’aikata da kuma rashin biyan wasu nasu albashin.
A ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu ne aka wayi gari ma’aikatan jihar suka fara ƙorafe-korafe kan cewa sun samu albashinsu amma bai cika ba kamar yadda suka saba karɓa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa an kuma umurci Salisu Mustapha da ya ajiye mukaminsa na Babban Sakatare Sakatare na Establishment, a karkashin Ofishin Shugaban Ma’aikata, domin a gudanar da bincike ba tare da tangarda ba.
Kuna iya karanta labaranmu a nan
Domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki, gwamnan ya amince da nadin Malam Umar Muhammad Jalo, Babban Sakatare na REPA, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riƙo, har sai an kammala binciken da ake yi.
Gwamna Yusuf ya kara jaddada matsayinsa na cewa ba zami lamunci duk lamarin da ya shafi almundahana ba, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci mummunan sakamako.
An ƙaddamar da kwamitin da zai yi bincike kan lamarin, wanda aka sanya Abdulkadir Abdussalam ya jagoranta, kuma an ba da wa’adin kwana bakwai don gano tushen inda aka samu kura-kurai da matsalolin, sannan a gabatar da sakamakon binciken.
A farkon wannan watan ne aka nada Salisu Mustapha a matsayin shugaban ma’aikata na riko, biyo bayan hutun jinya da aka bai wa babban shugaban ma’aikatan Abdullahi Musa wanda yanzu haka yake jinya a kasar Indiya.