Hukumomi sun ce adadin mutanen da aka kashe a Goma da kewaye a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya zarta 8,500 tun daga watan Janairu, lokacin da 'yan tawayen M23 suka tsananta fada da dakarun gwamnati tare da kwace birnin.
Ministan lafiya Samuel-Roger Kamba ya ce a ranar Alhamis fiye da mutane 5,700 ne suka ji raunuka.
"Mun riga mun binne fiye da mutume 8,500 a birnin Goma. Har yanzu akwai gawarwaki kimanin 30 a dakin ajiyar gawa," kamar yadda Kamba ya shaida wa manema labarai yayin wani taron manema labarai dangane da alkaluma da aka yi na baya bayan kan matsalar jinƙai a Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
"A cikin kwanaki biyun da suka gabata kadai, mun kwaso gawawwakin mutum 23 da aka kashe tsakanin 23 zuwa 25 ga watan Fabrairu."
Kamba ya ce gwamnati ta kuma yi Allah wadai da tilasta wa matasa shiga ayyukan 'yan tawaye, yana mai cewa "ya zuwa yanzu manyan motoci hudu sun debo matasa domin tilasta musu shiga cikin abokan gaba."
Karin mutum 1,500 sun mutu
A farkon makon nan, firaministan ya ce an kashe a kalla mutum 7,000 tun daga watan Janairu, wanda ya kai a kalla adadin wadanda suka mutu ya karu 1,500.
A ranar 27 ga watan Janairu, 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, sun yi ikirarin ƙwace birnin Goma, yayin da gwamnatin da ke da hedkwata a Kinshasa ta yi ikirarin cewa dakarun Rwanda na nan a birnin.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu bama-bamai biyu suka tashi a wani gangamin 'yan tawayen M23 a garin Bukavu, wani birnin da kungiyar masu dauke da makamai suka ƙwace a gabashin DRC, inda suka kashe akalla mutane 11 tare da jikkata 65.
Kungiyar M23 ta ce tana kare muradun 'yan kabilar Tutsi 'yan tsiraru na Congo, wadanda suka ce ana nuna musu wariya saboda alakarsu da kabilar Tutsi ta Rwanda.